1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin mayakan IS na Iraki da gallaza wa mutane

September 2, 2014

Majalisar Dinkin Duniya za ta binciki kisan da mayakan IS na Iraki ke yi ga mutanen yankin arewacin kasar

https://p.dw.com/p/1D58j
Hoto: picture alliance/AP Photo

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya za ta tura masu bincike kan laifuffukan yaki da ake zargin mayakan masu neman kafa daular Islama ta aiwatarwa.

Kasashen Faransa da Iraki suka gabatar da kudirin. Mataimakiyar shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, Flavia Pansieri, ta ce jami'an hukumar da ke kasar ta Iraki za su ci gaba da tattara shaida kan yadda 'yan kungiyar ta IS ke cin zarafin mutane wajen kisa, da tilasta musu sauya addini, garkuwa da mutane da amfani da mata a bayi da sule lalata da su.

Tun farko kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mayakan IS na kasar ta Iraki da aiwatar da kisan kare dangi wa kananan kalibu na arewacin kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu