1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da Allah wadai da kisan baki a Afirka ta Kudu

Ahmed SalisuApril 18, 2015

Shugabannin kasashen duniya sun nuna takaicinsu dangane da yadda ake cigaba da kisan baki da washe dukiyarsu a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1FARp
Südafrika Fremdenfeindliche Ausschreitungen
Hoto: Reuters/R. Ward

Kasashen duniya da kungiyoyi na kare hakkin bani Adama na cigaba da nuna takaicinsu dangane da yadda ake cigaba da kisan baki da washe dukiyarsu a wasu sassa na Afirka ta Kudu.

Wadanda wannan lamari ya shafa sun zargi mahukuntan kasar da gaza tabuka komai wajen kawo karshen kisan 'yan kasashen wajen a kasar duba da yadda wadanda ke aikata hakan ke cin karensu ba babbaka.

Wannan yanayi da ake ciki a kasar ya sanya wasu kasashen musamman ma na Afirka kwashe al'ummarsu daga kasar don gudun kada su fada tarkon masu kyamar bakin.

A wasu kasashen kuwa ciki har da Zimbabwe, mutane ne suka yi zanga-zanga ta nuna rashin amincewarsu da kisan na baki 'yan Afirka a kasar, inda suka bukaci kawo karshen batun cikin hanzari.