1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da zabe a wasu wurare a Najeriya

Muntaqa AhiwaMarch 29, 2015

Mahukunta a Najeriya sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kada kuri'a a akalla rumfunan zabe 300 na kasar

https://p.dw.com/p/1EzFG
Nigeria Wahlen Scanner Daumenabdruck
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar, an ci gaba da zabukan ne a yau Lahadi don baiwa saura damar damawa kamar kowa, ta kuma amince da kura-kuran da aka samu na na'urorin tantance masu zabe a jiya.

Najeriya na da rumfunan zabe dubu 150 ne a fadin kasar, kamar mahukunta suka tabbatar.

Zaben na wannan lokaci dai ya ci karo da wasu hare-haren da aka danganta da mayakan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, wadanda suka halaka akalla mutane 41, sai kuma wasu mutanen uku ciki har da Soji guda da aka halaka a jihar Rivers da ke a kudancin kasar.