1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi 'yan Jihadi da bata sunan Islama

August 19, 2014

Wani babban malamin addinin Islama na Saudiyya ya bayyana cewa addinin ba shi da manyan makiya kamar masu kaifin kishin addini irin su al-Qaida da IS.

https://p.dw.com/p/1CxBS
Kronprinz Abdullah von Saudi Arabien
Hoto: AP

Babban limamin Saudiya ya bayyana a ranar Talatar nan cewa addinin Islama ba shi da manyan makiya kamar masu kaifin kishi da akida irin ta al-Qaida da dakarun IS domin Musulmai su ke fara cutuwa da ayyukansu.

Mufti Sheik Abdul-Aziz Al-Sheik da yake wa jamaa bayani yace taaddanci bashi da gurbi cikin addinin Islama, kuma babbar barazanar da suke da ita, ita ce suna amfani da wasu kalmomi na addinin Islama wajen aiwatar da ayyukansu na rarraba kan musulmi.

Tuni dai Sarki Abdallah na Saudiyyar ya yi ta kira ga babban malamin da ya fito fili ya yi Allah wadai da ayyukan masu kaifin kishin addinin na Islama tun bayan da gwamnatin ta haramta shiga fada ga 'yan kasar a rikicin kasashen waje.

Ya zuwa yanzu dai duk wasu malaman addini da suka ki yin Allah wadai da ayyukan na masu kaifin kishin addinin Islama a waazin su na jumaa-jumaa a kasar ta Saudiyya na iya fiskantar wasu matsaloli da suka hadar da kwace musu lasisi na yin waazi.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mouhammadou Awal Balarabe