1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu jinkiri a zaben kasar Lesotho

Usman Shehu Usman February 28, 2015

'Yan Lesotho kusan miliyan biyu na kada kuri'a da nufin zaben sabbin 'yan majalisa watanni shida bayan yunkurin juyin mulki da ya ci tura.

https://p.dw.com/p/1EjAY
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Mohamed

Ana can ana gudanar da zaben 'yan majalisa a kasar Lesotho, watanni shida bayan da 'yar mitsitsiyar kasar da ke yankin Kudancin Afirka ta fada cikin rikicin siyasa biyo bayan yunkurin juyin mulki da sojoji suka yi. An samu jinkirin fara kada kur'ia a runfunan zaben kasar 2000, wanda 'yan sanda masu kwance bama-bamai da karnuka ke zagayawa don tabbatar da cewa zaben ya gudana ba tare da tashin hankali ba.

Lesotho dai ta na karkashin jogorancin masarauta ne, inda take da iyaka da kasar Afirka ta kudu a ko wane gefe. Tun bayan yunkurin kifar da gwamnatin firaminista Thomas Thabane, aka dakatar da majalisar dokoki domin gudun tsigeshi firaministan idan ta yi zama.

A Shekara ta 2012 ne dai fiministan ya jagoranci wasu kananan jam'iyyu wajen kafa gwamnati. Kimanin mutane miliyan 1.200 biyu ne aka yi wa rijista don kada kuri'a.