1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon shugaban kasar Indunusiya

October 20, 2014

Joko Widodo ya yi alkawarin kawo sauye-sauye wa kasar Indunusiya bayan rantsuwar kama aiki.

https://p.dw.com/p/1DYjO
Hoto: Reuters//Darren Whiteside

Sabon shugaban kasar Indunusiya Joko Widodo ya yi rantsuwar kama aiki, inda ya nemi 'yan adawa su hada hanu tare wajen ciyar da kasar gaba.

Widodo dan shekaru 53 da haihuwa ya lashe zaben da aka gudanar a watan Yuli, amma akwai tsoron yadda 'yan adawa suka kane-kane a majalsiar dokoki, haka zai iya yanjo cikas wa sauye-sauyen da sabon shugaban zai aiwatar.

Sabon Shugaban kasar ta Indunusiya Joko Widodo ya karbi madafun iko daga hannun Susilo Bambang Yudhoyono wanda ya kammala wa'adin mulkinsa. Widodo zai mulki kasa mai mutane milyan 250, da suke rayuwa a tsibirai fiye da 17,000.

Mawallafi: Suleiman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe