1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana fita a Kaduna

July 23, 2014

Zartar da wannan doka da Gwamnatin Kaduna ta yi, ya biyo bayan tagwayen harin bama bamai, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane masu yawa.

https://p.dw.com/p/1ChCS
Anschlag Autobombe in Kaduna Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Bam din farko wanda ya tashi a titin nan na Alkali Road da ke tsakiyar garin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane kimanin sha biyar yayin da ya jikkata wasu da dama da kuma lalata motocin da ke gefen hanya daura da inda abin ya faru.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dau alhakin kai harin sai da ana zaton an kai shi ne da nufin hallaka malamin addinin Islaman nan Sheikh Dahiru Bauchi kasancewar bam din ya tashi ne daidai lokacin da jerin gwanon motocinsa ke wucewa.

A yayin da bam na biyu da ya tashi a kasuwar Kawo da ke cikin garin Kaduna, an yi nufin kai shi ne a kan ayarin motocin tawagar jigo a jam'iyyar adawa ta APC kuma tsohon dan takarar kujerar shugabancin Najeriya Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Ahmed Maiyaki ya ce, kafa dokar hana fita da awa 24 na da nufin tabbatar da doka da oda a cikin fadin garin.

Jihar Kaduna dai kamar sauran jihohin arewacin kasar ta sha fama da tashin hankali da fashewar bama-bamai wanda galibi ake alakantawa da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai.

Ana iya sauraron sauti daga kasa

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar