1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta tura soji kan yaƙi da cutar Ebola a yammacin Afirka

Yusuf BalaSeptember 16, 2014

Dakarun soji 3,000 za su tafi zuwa ƙasashen na yammacin Afirka dan su ba da agaji da horo kan kula da lafiya da shirin tsaftar muhalli cikin yaƙi da Ebola.

https://p.dw.com/p/1DCnv
Obama - Rede an die Nation
Hoto: Reuters

Shugaba Barack Obama na Amirka a ranar Talatan nan zai bayyana wani shiri da zai kawo sauyi a yaƙin da ake yi da annobar Ebola a ƙasashen da ke yammacin Afirka.

Fadar White House ta bayyana cewar shugaba Obama zai ziyarci cibiyar da ke da alhakin kula da rashin bazuwar ƙwayoyin cuta da ke Atlanta, inda zai gana da shugabannin jami'an lafiya, sannan ya yi wannan sanarwa da za ta zama babbar shela a yaƙin da ake da wannan cuta ta Ebola a duniya, wacce tuni ta kashe mutane 2,400.

Wannan sanarwa dai na zuwa ne adaidai lokacin da ake samun ci gaban fargabar bazuwar wannann cuta da tuni ta mamayi kasashen Laberiya da Saliyo da Najeriya da Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango.