1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta dukufa kan yaki da Ebola a Afirka

Salissou BoukariSeptember 15, 2014

A wani mataki na neman kawo karshen matsalar cutar Ebola a yammacin Afirka, Shugaban Amirka Barack Obama zai fitar da wani tsari kan wannan batu.

https://p.dw.com/p/1DCZW
Hoto: Reuters

Shugaban kasar Amirka Barack Obama, na shirin shigar da bukatar wasu kudade da yawansu ya kai Dalar Amirka miliyan 88 ga Majalisar dokokin kasar, domin yaki da cutar Ebola a yammacin Afirka.

A ranar Talatar shugaban zai bayyana tsarin nasa kan wannan batu, yayin wata ziyara da zai kai a ma'aikatar kula da bincike da kuma rigakafin cututtuka da ke birnin Atlanta a cewar jaridar Wall Street. Ana sa ran tsarin na Obama, zai kasance ne kan batun aikewa da manyan asibitocin tafi da gidanka, tare da aikewa da kwararrun likitoci da kayan aiki. Sannan kuma da batun bayar da horo ga jami'an kiwon lafiyar kasashe daban-daban da ke fama da wannan annoba.