1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta bawa Lebanon tallafin kayan yaki

August 29, 2014

An mika kashin farko na tallafin makamai ga gwamantin Lebanon don agaza mata wajen kare kanta daga barazana da ta ke fuskanta daga mayakan kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/1D3eG
Libanon Panzer Tripoli Syrien
Hoto: Reuters

Da sanyin safiyar yau ne aka baje kolin makaman a wani sansanin sojin saman kasar ta Lebanon da ke Beirut wadanda suka hada da bindigogi da rokoki da kuma makaman lalata tankokin yaki.

A watan da ya gabata dai jakadan Amirka a kasar David Hale ya ce mahukuntan Lebanon suka nemi wannan tallafi bayan da mayakan na IS suka yiwa wani gari da ke kan iyakar kasar da Siriya tsinke inda suka hallaka soji da dama da kuma yin garkuwa da wasu.

Amirka dai na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen tallafawa Lebanon ta fuskar sojin don daga shekara ta 2006 zuwa yau Washington ta baiwa Beirut din tallafi ta fuskar soji da kudinsu ya kai sama da dala miliyan dubu daya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman