1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ke kan gaba kan harkar jiragen sama

September 8, 2014

Kasar Amirka ke kan gaba a jerin kasashen duniya masu yawa da ke kera jiragen sama.

https://p.dw.com/p/1D7f7
Hoto: picture-alliance/dpa

Akwai kasashen duniya yanzu masu yawa da ke kera jiragen sama a duniya, da suka hada da na fasinja, da dakon kaya, da kuma na sojoji. Kasar Amirka ke kan gaba wajen kera jiragen sama, kuma a kasar aka fara kera jiragen sama a farkon shekarun 1900.

Akwai kamfanin kera jiragen sama na Faransa, wanda mallakin kasashen Faransa da, Jamus da kuma Birtaniya. Sannan ana yi wani sashe na jirgin a kasar Jamus. Ita ma kasar Brazil tana da kamfanin kera jiragen sama, haka Rasha da Canada. Kasar Italiya tana da kamfanin kere jiragen sama.

Kasashen Afirka babu wata kasa da ke kera jiragen sama, amma kasashe kamar Habasha da Masar suna da wuraren gyara da suka yi fice.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal