1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Almara a Afirka domin al’adu da zaman lafiya

August 11, 2010

Labarai ne na barkwanci, ban dariya ko ɓacin rai, ɗimautarwa ko annashuwa.

https://p.dw.com/p/OiG1
Hoto: LAIF
Almara na jan hankali masu sauraro a dukkan matakai. Labarai goma da aka zaɓa ba wai kawai na nishaɗantarwa ba ne, amma suna nunar da mutuntaka, ilimantarwa da kuma hikimomi da aka gada.

A nahiyarmu ta Afirka, har yanzu ana darajawa al'adar nan ta yin tatsuniya. Domin yana ɗaya daga cikin hanyoyin darajawa al'dun garjiya.

Da yawa daga cikinmmu za su iya tuna irin labarai ko kuma tatsuniyoyi da iyaye ko kuma kakanninmu ke faɗa mana a kan abubuwan tarihi. Kazalika Ndiaye Ibrahima daga Senegal. A waɗannan Almara guda goma da za ku ji a wannan shirin, sun kasance irin tatsuniyoyi ne da ya ji daga wurin kakarsa domin inganta fahintar juna da zaman lafiya.

Dabbobi dai suna taka muhimmiyyar rawa a cikin almara-manya da ƙanana, mai ƙarfi da malalaci, jarumi da matsoraci. Muna ɗauke da labarin Zaki, Kura, Tattabara, Giwa, Maciji da dai sauransu da irin kasadarsu. Yanayi da za su tsinci kansu, da rikicin da su da kansu za su warware, suna kama dana mafi yawa daga cikimmu.

Ana iya sauraron shirin Ji Ka ƙaru a harsuna shida: Turanci, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portugues da Amharik. Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ke tallafawa shirin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar