1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Saudiya na jefa fararen hula cikin tasku

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 18, 2015

A kallah mutane 27 ne suka rasa rayukansu a birnin Taez na kasar Yemen a hare-haren da Saudiya ke kaiwa 'yan tawayen Huthi da suka kwace iko da wasu manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/1FAZe
Hare-haren Saudiya a Yemen
Hare-haren Saudiya a YemenHoto: Reuters/Str

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan yaki da Saudiya ke jagoranta yayin da dubun-dubatar iyalai suka kauracewa matsugunansu inda kuma sojojin Saudiyan shida suka rasa rayukansu. Majalisar ta kara da cewa ana bukatar kudi da yawansu ya kai dalar Amirka miliyan 274 domin bada agajin gaggawa ga al'ummar Yemen din da yaki ya rutsa da su. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa tuni kasar Saudiya ta sha alwashin bayar da baki dayan wadannan makudan kudaden.Tsahon makawanni uku ke nan dai kasar ta Saudiya ke jagorantar kawayenta suna yin barin wuta a kasar ta Yemen musamman a yankunan da 'yan tawayen na Huthi da ke zaman Musulmi mabiya Shi'a suke rike da madafun iko, hare-haren kuma da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hular kasar.