1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙauracewar ƙwararru daga ƙasashensu na asali

June 19, 2012

Masu basira a kowane lokaci sukan sami aikin yi, idan kuma basu samu ba a ƙasashensu na haihuwa ko albashin bai gamsar da su ba sai su ƙaurace zuwa wata ƙasa.

https://p.dw.com/p/15Hpt
health; medicine; doctor; healthcare; medicalcare; surgeon; stethoscope; hospital; portrait; x-ray; radiography; radiograph; checking; examining; man; black; african; African-American; male; cheerful; joyful; ethnicity; culture; diversity; 30 years old; looking at camera; office; working; student; indoors; health; medicine; doctor; healthcare; medicalcare; surgeon; stethoscope; hospital; portrait; x-ray; radiography; radiograph; checking; examining; man; black; african; african-american; male; cheerful; joyful; ethnicity; culture; diversity; 30 years old; looking at camera; office; working; student; indoors goodluz - Fotolia.com
Hoto: Fotolia/goodluz

A yanzu haka dai kauracewar matasa masu illimi mai zurfi daga ƙasashe masu tasowa na zaman wata babbar matsala, a dalilin haka ne ƙasashen ke neman hanyoyin cin moriyar wannan ƙwarewar da suka mallaka a maimakon yin asararsa

Babban bankin duniya na ƙiyasin cewa Afirka na asarar kimanin mutane dubu 23 na mutanen da ke da illimi mai zurfi a kowace shekara.

Wata cibiyar binciken Kanada, ta ce a ƙasashen da ke yankin Kudu da Sahara kaɗai sukan sami giɓi daga milliyan dubu biyu na dalan Amurkan da sukan kashe kan likitoci waɗanda suka ɗauki nauyin karatunsu, sakamakon ƙauracewar da suke yi da zarar sun kammala karatu zuwa ƙasashen ƙetare.

Haƙiƙa wannan bai dace ba, amma kuma akwai batun kuɗin da waɗannan 'yan ci ranin ke samu a ƙasashen waje wanda suke aikawa iyalai da abokansu na gida. Idan har aka gwada yawan wanna kuɗi da su kan aika sai a ga ya ninka ma kuɗin tallafin da ƙasashe masu manyan masana'antu kan tura kuma wannan kuɗi sai ya zama na ƙasa baki ɗaya.

Har wa yau, bai kamata mutun ya kawar da kai daga wani adadi na waɗannan masu ci ranin waɗanda kan dawo gida bayan shekaru da dama, su yi aiki ko kuma ma su yi amfani da kuɗaɗensu a matsayin jari ma ayyukan bunƙasa ƙasa ba. Irin wannan ne ɗaya daga cikin mahimman hanyoyin da zasu ƙalubalanci wannan ƙauracewar ta neman riba da illimi ko kuma dabarun da mutun ke da shi.

Schule in den Slums von Nairobi
Hoto: picture-alliance/photoshoot

Kauracewa mai amfani ga masu gudun hijira

Stefan Angenendt wani ma'aikaci a wata gidauniyar kimmiya da siyasa ya sanya ido kan wannan sabon salo na wani tsawon lokaci yanzu kuma ga ƙarin bayanin da ya yi:

"Wannan ya danganci irin damammaki masu inganta rayuwar da suke hange. Akwai damar tafiya a sauƙaƙe, waɗanda suka fita, sun riga sun samar da hanyoyin cuɗanya da hulɗa da mutane daban-daban ta haka ne ma ƙauracewar ya zama da sauƙi saboda yawancinsu sukan je inda suka riga suka san mutane ne"

A dalilin haka ne ma ake fitar da wani tsari ga waɗannan masu illimi mai zurfi waɗanda ke sha'awar zuwa Jamus da ma sauran kasashe dan kansu. A wannan tsari, wajibi ne ya kasance mutun na da manufar komawa gida a cewar Angenendt, banda haka kuma wanda ke da niyyar komawa yana buƙatar goyon baya kamar shawarwari, shirye-shiryen tallafi wanda zai taimaka wajen farawa daga farko a can a gida

Tsarin tallafawa kwararru

Manufar tallafawa ƙwararrun zai amfane mutane ta hanyoyi guda uku a cewar Gunilla Finke, shugabar gidauniyar Jamusa a kan tabbatar da cuɗanya da kuma kula da 'yan gudun hijira, kuma a cewarta tun farko mai gudun hijiran ne ke da riba:

"Zai yi riba fiye da inda ya fito. Zai kuma ci-gaba da illimantar da kansa ta yadda zai sami ƙarin takardu da ƙwarewa daga ƙarshe. Haka nan kuma yana iya ƙulla ƙawance da ƙungiyoyin tallafi waɗanda zasu iya taimaka masa da zarar ya koma gida"

Dr. Gunilla Fincke vom Sachverständigenrat deutscher Stiftungen für Integration und Migration (SVR). Copyright: David Ausserhofer 2012
Dr. Gunilla FinckeHoto: David Ausserhofer

Na biyu kuma Jamus zata ci moriyar zuwansa, saboda ya kan zo da irin ƙwarewar da take buƙata, amma daga ƙarshe ƙasarsa zata fi cin moriya saboda bayan wani tsawon lokaci zai sami ƙarin illimi da kuma ƙwarewa a fanin da yayi aiki. To sai dai duk wannan a rubuce ya ke, a zahiri abun na da wuya idan aka zo aikin ya kan kasance wani abu daban

Kalubalen nasarar shirin tallafin

"A zahiri babu sauƙi sosai a yi nasarar samun waɗannan abubuwa uku. A yanayin buƙatar ma'aikata a Jamus yanzu, ana neman waɗanda ke da ƙwarewa ne sosai kuma ba'a duka ƙasashen za'a iya ɗauka ba. Daga ƙasashen da mutanen ke kwararowa, mafi yawa suna da matsakaici ne ko kuma ƙaramin ƙwarewa, a yayinda su kuma Jamusawa son mutane masu ƙwarewa su ke yi, kuma hakan ba zai zo ɗaya ba"

Wannan shiri dai yana da kamar wahala, sakamakon ra'ayoyi mabanbanta da ake da su dangane da shi a nan Jamus, 'yan siyasan ƙasar da dama basu goyon bayan kwararowar baƙi domin fargabar ɓacin ran masu zaɓe, domin sun san cewa mutane da yawa na gudun rasa nasu guraben aikin. Manyan kamfanoni a ɓangare guda kuma sun fi so a rage tsaurin yawan karatun da ake buƙata, domin a ko da yaushe suna neman ƙwararrun ma'aikata.

Mawallafa: Klaus Dahmann / Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal