1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Mata masu juna biyu da matsalolin kiwon lafiya

May 14, 2024

Masu juna biyu a Najeriya sun koka da yadda magunguna da sauran kayayyakin kula gami da taimakon jarirai suka yi tsada inda suka nemi hukumomi su dauki matakai don ceto rayuwarsu da jarirai da suke shirin haifa.

https://p.dw.com/p/4fq2J
Mai juna biyu
Mai juna biyuHoto: BARBARA DEBOUT/AFP

Sai dai wasu gwamnatoci sun dauki matakin saukakewa mata masu juna hanyoyin da za su samu magunguna cikin sauki ko kuma ma kyauta a wasu jihohin. Mata da juna biyu a Najeriya sun koka da yadda magunguna gami da sauran kayan kula da taimakawa jariransu  inda duk sun yi tsada, abin da ya saka suka nemi hukumomi su dauki matakan da suka dace don ceto rayuwarsu da jarirai da suke shirin haifa.

Karin Bayani: Najerriya: Yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Matsalolin faduwar darajar Naira da kuma tsadar makamashi da su ka haifar da tashin farashin kayayyakin masarufi da abinci har da magunguna lamarin da ya shafi masu neman lafiya a kusan duk jihohin Najeriya. Dubban Mata da ke da juna biyu sun ce ba sa iya sayen da yawa daga cikin magungunan da likitoci suka rubuta musu wadanda wasu na taimakon su da jarirai da ke cikin su wanda ke rashin samun sayen suka iya shafar rayuwarsu. Wannan damuwa da mata masu juna biyu suke nunawatare da mazajensu gami da masana lafiya da masu fashin baki kan yadda ya kamata a magance matsalar tsadar magungunan. Domin samun sauki magungunan zai yi tasiri wajen ceton rayuwar matan gami da jarirai.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta bakin ministan lafiya ta ce suna bakin kokari wajen an saukake tsadar magunguna inda wasu jihohi suka fara ba da magunguna kyauta ga masu juna biyu don saukake musu wannan hali da ake ciki.