1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Kotun Chadi ta ce Deby ne ya lashe zabe

May 16, 2024

Kotun tsarin mulkin Chadi ta tabbatar da janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar tun a zagayen farko, inda ya samu kaso 61 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/4fxDd
Tschad N'Djamena | Präsident Mahamat Idriss Deby
Hoto: AFP

Wannan hukunci na kotun tsarin mulkin Chadin da ya tabbatar da nasarar ta shugaban gwamnatin mulkin sojan rikon kwaryar ya samu a zaben da aka gudanar a ranar shida ga wannan wata na Mayu da muke ciki, ya kawo karshen mulkin sojoji na shekaru uku. Kazalika kotun tsarin mulkin ta Chadi ta yi watsi da kararraki da kuma bukatar da dan takarar adawa Succes Masra ya mika mata, na a soke zaben kan dalilan zargin tafka magudi da aringizon kuri'u. A sakamakon karshe da kotun ta fitar dan takarar adawar mai shekaru 40 a duniya ya zo a matsayi na biyu da sama da kaso 18 cikin 100, yayin da tsohon firaministan kasar Albert Pachimi Padacke ya zo na uku da sama da kaso 16 cikin 100. Wannan sakamako da kotun ta tabbatar dai ba ya da babanci da sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta Chadi ta fitar a ranar tara ga wannan wata na Mayu, lamarin da ya bar baya kura.