1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Allon talla ya kashe mutum hudu a Indiya

May 13, 2024

Mutane hudu sun rasa rayukansu, akalla 60 kuma sun ji raunuka sakamakon fadowar wani allon talla biyo bayan iska mai karfi a Mumbai cibiyar kasuwancin Indiya.

https://p.dw.com/p/4foGn
Ambaliya a Indiya
Ambaliya a IndiyaHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Allon ya fadi ne a wani gidan mai da ke gabashin birnin na Mumbai a Indiya lamarin da ya haddasa makalewar mutane da dama.

Mutane 60 da aka ceto zuwa yanzu suna kwance a asibiti suna karbar magani kamar yadda wata sanarwa da hukumomin birnin suka fitar ta nuna.

Ambaliya ta kashe rayuka a Indiya

'Yan sanda sun wallafa a shafinsu na X cewa allon na da tsawo da fadin mita 70 ga 50.

Iska mai karfi tare da mamakon ruwan sama sun afka wa birnin Mumbai a ranar Alhamis kuma sun tuge bishiyoyi da dama lamarin da ya ci gaba da haddasa tsaiko a sassan daban-daban.