1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
May 17, 2024

Yayin da aski ke kara gabatowa gaban goshi a zaben kasar Afirka ta Kudu, har yanzu tana kasa tana dabo game da takarar tsohon shugaban kasar Jacob Zuma

https://p.dw.com/p/4g0ve
Jaridun Jamus
Jaridun JamusHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali kan siyasar Gambiya a karkashin sharhinta mai ta ken: "Shekaru 20 a gidan yari ga tsohon ministan cikin gida na Gambiya". Jaridar ta ce kotun hukunta manyan laifuka ta tarayya ta kasar Switzerland ta yanke wannan hukuncin ne bayan da aka samu Minista Ousman Sonko da laifukan da ke da dangantaka da cin zarafin bil adama bayan shekaru da dama na bincike.

A watan Janairun 2017 ne aka kama Ousman Sonko a cibiyar neman mafaka ta 'yan gudun hijira a gundumar Bern ta kasar Switzerland bayan da wani dan kasar Gambiya ya gane shi, lamarin da ya sa kungiyar kare hakkin dan Adam ta Geneva ta shigar da kara a gaban kotu. Shafuka 150 ne dai takardar tuhumar Sonko ta kunsa bisa laifukan da suka hada da kashe-kashe da azabtarwa da kuma fyade a lokacin da yake rike da  matsayin babban jami’in ‘yan sanda da kuma ministan cikin gida. Kafofin yada labarai na kasar Gambiya sun shafe makonni suna bin diddigin yadda shari'ar ta gudana a kotun da ke Bellinzona, don yin tir da mulkin danniya na tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob ZumaHoto: AP/picture alliance

Ita kuwa die tageszeitung ta yi tsokaci kan siyasar Afirka ta Kudu inda ta nunar cewar "Komai ya ta'allaka ne a kan Jacob Zuma" da ke zama tsohon shugaban wannan kasa. Jaridar ta ce makonni biyu gabanin zaben Afirka ta Kudu, har yanzu ba a san ko za a bar tsohon shugaban kasar Zuma ya tsaya takara a karkashin sabuwar jam'iyyarsa ta siyasa ba ko a'a. Yayin da kotun tsarin mulki ke tattaunawa don yanke hukunci a akan wannan batu, magoya bayansa na nuna doki da murna saboda suna ganin cewar ana yi masa yarfen siyasa ne domin hana shi tsayawa takara.

die tagaszeitung ta kara da cewa, bisa ga kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu, ana iya yanke wa mutamin da aka samu da laifi cin hanci hukuncin daurin rai da rai, amma dai aka yanke wa Jacob Zuma hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari. Yanzu haka ma, ba shi damar rike mukaman gwamnati, lamarin da ya sa tun da farko hukumar zaben kasar ta cire dan siyasar daga jerin sunayen 'yan takara. Zuma ya jagoranci Afirka ta Kudu a matsayin shugaban kasa daga 2009 zuwa 2018, kafin a sauke shi ne saboda zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Mashigin Rafah a iyakar Gaza da Masar
Mashigin Rafah a iyakar Gaza da MasarHoto: GIUSEPPE CACACE/AFP via Getty Images

A nata bangaren Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo rikicin Gabas ta Tsakiya inda ta ce Masar ta mayar da martani ga farmakin da Isra'ila ta kai a Rafah ta Zirin Gaza ta hanyar toshe mashigar kan iyaka, wacce Alkahira ta saba amfana ba sau daya ba sau biyu ba. Ita kuwa Neue Zürcher Zeitung ta nunar da cewar harin na Rafah na Isra'ila ya haifar da takaddama da Masar tare da haifar da guna-guni daga bangaren sojojin sakamakon rashin sanin alkiblar da aka fuskanta ne. Ita kuwa Welt Online ta dasa ayar tambaya tana mai cewa "Me ya sa Masar ke yin illa ga yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila?. Ta ce Masar ta bi sahun Afirka ta Kudu kan zargin kisan kiyashi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya - har ma tana son soke yarjejeniyar zaman lafiya idan Isra'ila ta kara kaimi kan Rafah.

A fannin alakar Jamus da kasashe masu tasowa kuwa, Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta mai taken "BMW ya yarda da matsalolin muhalli da ya haifar da tsaiko a aikin hakar ma'adinin cobalt a Maroko." Jaridar ta ce bayan bincike guda biyu, kanfanin da ke kula da hako ma'adinan ya yi alkawarin gyara kura-kuran da aka tafka, amma kamfanin kera motocin na Jamus na son ci gaba da samar da cobalt na motocinsa masu amfani da wutar lantarki daga Maroko.

Hotunan tauraron dan Adam sun nuna cewa an gina sabbin ramuka a kudancin ma'adanin, lamarin da ke nuna cewar shara na haddasa gurbacewar ruwa a magudanan ruwa. Amma kanfanin BMW ya gudanar da bincike guda biyu a karkashin wasu kamfanoni biyu na waje bayan zargin da aka yi masa cewa yana cutar da  lafiyar ma'aikata tare da rashin alkinta muhalli a cibiyar hako ma'adinin cobalt a Maroko. Amma die tageszeitung ta ce BMW ya sanar cewa zai inganta salon gudanar da aikinsa a wannan kasa don samar da sanadarin na cobalt